rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Niamey

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar ta daure ‘Yan Sanda uku da suka ba dalibi kashi

media
A shekarar 1990 ne Jami'an tsaron Nijar suka kashe wasu dalibai uku Boureima Hama-AFP

Wata Kotu a Nijar ta yankewa wasu ‘Yan Sanda uku hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsu da laifin dukan wani dalibin jami’a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanga a Niamey.


Kotun ta kuma umurci ‘Yan Sandan su biya tarra sefa miliyan 15 kwatankwacin yuro 23,000 ga dalibin da suka jikkata.

Wani faifan bidiyo da aka dauka ranar gudanar da zanga zangar ya nuna ‘Yan Sandan guda uku na dukan dalibin da suka kama a bayan mota.

‘Yan sanda sun yi arangama da daliban da gudanar da zanga-zangar a watan Afrilu a Niamey.

A watan Fabrairun 2016 daliban Jami’a sun kaddamar da wata babbar zanga-zanga domin tuna kisan wasu dalibai guda uku da Jami’an tsaron Nijar suka yi shekaru 26 da suka gabata.