Isa ga babban shafi
Tanzania

Tanzania ta gurfanar da mutanen da suka kashe Mayu

Hukumomin Tanzania sun gurfanar da wasu mutane 32 a gaban kotu inda ake tuhumar su da laifin kashe wasu mata 5 da kuma kona gawarsu kan zargin cewar mayu ne.

Yankin Marangu da ke kusa da tsaunin Kilimanjaro a Tanzania
Yankin Marangu da ke kusa da tsaunin Kilimanjaro a Tanzania Marjorie Hache
Talla

Mai gabatar da kara Melito Ukongoji ya shaidawa kotun cewar wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a yankin Uchama kusa da tsaunin Kilimanjaro a ranar 27 ga watan Yulin da ya gabata.

Shugabar kungiyar lauyoyi mata a kasar Athanasia Soka, ta ce wannan shi ne karo na farko da aka gurfanar da mutanen da ake zargi da irin wannan kisan.

A ranar 4 ga Satumba ne mutanen za su gurfana gaban kotun yankin Nzega.

Sau da yawa ana kashe tsoffin mata ta irin wannan hanya saboda zargin cewar mayu ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.