Isa ga babban shafi
Angola

Jam'iyyar MPLA ta lashe zaben shugabancin Angola

Jam’iyyar da ke mulki a Angola ta lashe zaben da a ka yi a kasar abin da zai bai wa Joao Lourenco damar maye gurbin shugaba Jose Eduardo Dos Santos a matsayin shugaban kasar.

João Lourenço, zababben shugaban Angola
João Lourenço, zababben shugaban Angola REUTERS/Stephen Eisenhammer
Talla

Nasarar da Lourenco ya sama na nufin ci gaba da mulkin jam’iyyar MPLA wadda ke jan ragamar mulkin kasar tun bayan samun ‘yancin kai a 1975.

Har ila yau jam’iyyar ta samu gagarumin rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar mai kujeru 220, lamarin da zai bai wa zababben shugaban wanda tsohon soji ne damar tafiyar da mulkinsa a cikin sauki.

 

Angola dai kasa ce mai arzikin man fetur, to sai dai mafi yawan al’ummarta na rayuwa ne a cikin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.