Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An kashe dan jaridar Amurka a Sudan ta kudu

Dan Jaridar Amurka guda ya rasa ransa a Sudan ta kudu yayin wani rikici tsakanin sojin kasar da yan tawaye. Ofishin jakadancin Amurka ya ce dan jaridar mai suna Christopher Allen ya rasa ransa a lokacin da yake tsaka da daukar wani rikici daya barke tsakanin bangarorin biyu a Kaya dake kan iyakar kasar da Uganda.

shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Reuters
Talla

Ofishin jakadancin ya ce a jiya ne suka tabbatar da mutuwar dan jaridar Christopher Allen a rikicin tare da wasu mutum 18.

Sai dai kuma a wani martini da kakakin rundunar sojin Sudan ta kudu ya mayar, ya ce Christopher Allen baya daga cikin ‘yan jaridar da aka sahalewa daukar rahoton rikicin hasalima ya shigo kasar ne ta Uganda.

A bangaren guda kuma, ‘yan tawayen kasar cikin wata sanarwa da suka fitar sun yi tir da kisan na Allen tare da ayyana shi a matsayin take hakki da kuma karya doka da alfarmar kariya ga ‘yan jaridu yayin yaki.

Allen wanda ya yi aiki da kafar Aljazeera da kuma Vice News shi ne kuma ya rika daukar rahoton rikicin Ukraine.

Rikicin Sudan ta kudu dai ya samo asali ne tun daga lokacin da shugaba Salva Kiir ya zargi mataimakinsa Riek Machar da yunkurin juyin mulki a shekarar 2013 shekaru biyu bayan samun ‘yancin kasar.

Haka kuma rikicin ya raba kimanin mutum milyan hudu da gidajensu galibi mata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.