An bukaci mutane su kaucewa gidajensu a Yamai saboda ambaliya
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bukaci dubban mazauna yankin birnin Yammai da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa su kauracewa gidajensu sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da tafkawa a birnin.
Wallafawa ranar:
Gwamnan Yamai Soumana Ali Zataoua ya shaidawa al’ummar Yankunan da ke fuskantar barazanar ta kafar talabijin da su gaggauta ficewa daga gidajensu.
A karshen mako Katanga ta rufta da weani magidanci da dansa bayan ruwan sama da aka sashe sa’o’I ana makawa a Yamai.
Mazauna kusa da rafin Gountou-Yena a Yamai sun fi fuskantar barazanar ambaliyar, yayin da gidaje sama da 300 suka rushe a Gabagoura.
Tun watan Yuni akalla mutane 41 suka mutu a sassan Nijar sakamakon ambaliyar ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu