Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Iro Sani: Kan zargin gwamnatin Nijar bisa mika Sa'adi Ghaddafi ga mahukuntan Libya

Wallafawa ranar:

Gamnatin Nijar ta musanta zargin da lauyoyin iyalan tsohon shugaban Libya Mu’ammar Khaddafi suka yi, da ke cewa kasar ta mika Sa’adi Khaddafi ne ga mahukuntan Libya bayan da ta karbi dalar Amurka milyan dubu 4. Shi dai Sa’adi, ya gudu zuwa jamhuriyar Nijar ne bayan da aka kifar da gwmanatin mahaifinsa a shekara ta 2011, to sai dai bayan shekara daya gwamnatin Nijar ta sake mika shi a hannun gwamnatin Firaministan rikon kwarya Ali Zaidan, a wani yanayi da ake zargin cewa an bai wa manyan jami’an gwamnatin na Nijar makuddan kudade kafin su yi haka. Iro Sani, babban jami’i a gwamnatin ta jamhuriyar Nijar, ya musanta wannan zargi yayin tattaunawarsa da AbdoulKarim Ibrahin Shikal.

Saadi Kadhafi, da ga tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Ghaddafi.
Saadi Kadhafi, da ga tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Ghaddafi. Libération
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.