rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Mali Senegal Benin Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bukukuwan sallah a mafi yawan kasashen duniya a wannan juma'a

media
Raguna a birnin Dakar AFP/Seyllou

A wannan juma’a musulmi a sassa da dama na duniya sun fara gudanar da bukukuwan babbar sallah ko kuma sallar layya, bayan da mahajjatan suka sauka daga hawan Arafa.


A yammacin Afirka, kasashe kamar Najeriya, Benin, Mali da dai sauransu, ana bukukuwan babbar sallar ne a yau, yayin da a wasu kasashe irinsu Nijar da Senegal ke shirin gudanar da sallar a ranar asabar.

A sakon da ya aike wa al’ummar kasar dangane da zagayowar wannan rana, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, bayan ya yi wa mahajjata fatan alheri, ya bukaci illahirin ‘yan kasar da su jingine bambancin da ke tsakaninsu domin samar da hadin-kai, wanda ya ce shi ne tushen samar da ci gaba ga kowace al’umma.

Ana gudanar da bukukuwan sallar ne bayan da mahajjata suka sauka daga hawan Arafa sannan suka fara aikin jifar Shaidan a Mina, kusa da Makka.