Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Fursunoni 100 sun tsere daga gidan Yarin Cote d'Ivoire

Fursunoni akalla 100 ne suka tsere daga wani gidan yari dake kasar Cote d”Ivoire da safiyar jiya Lahadi.

Jami'an tsaron na sintiri a bakin gidan yarin kasar Cote d'Ivoire da fursunoni 100 suka tsere.
Jami'an tsaron na sintiri a bakin gidan yarin kasar Cote d'Ivoire da fursunoni 100 suka tsere. Gulf Times
Talla

Fursunonin gidan yari dake garin Katiola sun huda rufin dakunan su ne kafin samun damar tserewa.

Kafofin yada labaran kasar sun rawaito cewa duka fursunonin, magoya bayan wani jagoran rikicin da aka samu a gidan Yari ne a shekarar bara, wato Coulibaly Yacouba, wanda aka fi sani da Yacou le Chinois, wato ‘Dan China’.

A watan Fabrairu na shekara ta 2016 aka kashe shi, a yayin wani yunkuri da yayi na tserewa daga gidan yari dake Abidjan.

Tun a shekara ta 2012ake tsare da Coulibaly Yacouba, saboda zarginsa da aikata lafin kisa, kuma shi ne ya jagoranci yunkurin ficewa daga gidan Yarin.

Majiyoyi na cewa ta rufin kwanon dakunan gidan yarin fursunonin suka rika bulawa, suna kama gabansu.

Ko a farkon shekarar da muke ta 2017, an samu tarzoma a gidajen yarin kasar, to amma wannan shi ne na baya-bayannan da fursunonin suka tsere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.