rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Tarayyar Afrika Shari'a

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukuncin kotun Kenya daraja ce ga Afrika- Conde

media
Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika Alpha Condé Reuters / Ludovic Marin

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika, Alpaha Conde ya bayyana cewa, hukuncin da Kotun Kolin Kenya ta yanke na soke zaben Uhuru Kenyatta, wata daraja ce ga nahiyar Afrika.


A karon farko kenan da wata kotu a nahiyar Afrika ke soke sakamakon zabe kamar yadda aka gani a Kenya, in da Kotun Kolin kasar ta kuma bada umarnin gudanar da sabon zaben cikin kwanaki 60.

Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika, Alpha Conde, ya bayyana cewa wannan mataki, wata daraja ce ga Afrika da ta yi kaurin suna wajen tafka makudi, kuma hakan na nuna cewa, a yanzu demokuradiya ta samu gindin zama a nahiyar.

Conde ya kara da cewa, Kungiyar Tarayyar Afrika ta yaba da dattakun da bangarorin da ke adawa da juna suka nuna a Kenya, in da suka zabi shigar da kara a gaban kotu don magance rikici.

A cewar Conde, nan gaba Afrika za ta kai matakin da ake bukatar ta kai.

Jagoran ‘yan adawar Kenya, Raila Odinga wanda ya kalubalancin sakamakon zaben a gaban Kotun, ya yaba da hukuncin mai cike da tarihi.

Tuni dai shugaba Uhuru Kenyatta ya amince da hukuncin duk da dai ya caccaki alkalan kasar, tare da yin watsi da kiraye-kirayen ‘yan adawa na sauya jami’an hukumar zaben kasar.