Isa ga babban shafi
Mali

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama kan Mali

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taro gobe Talata domin amincewa da matakan sanyawa bangarorin dake karya yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali takunkumi.

Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.
Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Africatime
Talla

Kasar Habasha dake jagorancin kwamitin tace kasar Faransa ce ta gabatar da daftarin saboda barazanar watsi da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a shekarar 2015, da da wasu kungiyoyin ‘yan tawaye ke yi.

Karya yarjejeniyar da gwamnatin kasar Mali ta sanya hannu tare da hadin kan kungiyoyin dake dauke da makamai, wadanda a shekarar 2012 suka mamaye arewacin kasar, ya fara barazanar maida kasar cikin halin rashin zaman lafiya, wanda shi babban dalilin da ya sanya Faransa mika daftarin bukatar sanya takunkumin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.