Isa ga babban shafi
Llibya

Ministan wajen Faransa na ziyara a Libya

Ministan harkokin waje na kasar Faransa Jean-Yves Le Drain na gudanar da ziyara a kasar Libya inda ya bada tabbacin ganin Faransa ta taimaka don a warware rikicin siyasar da matsalolin rashin tsaro a kasar.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian yayinda yake jawabi a harabar Ofishin Firaministan kasar Libya a Tripoli.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian yayinda yake jawabi a harabar Ofishin Firaministan kasar Libya a Tripoli. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Jean-Yves Le Drain ya shaidawa fmanema labarai a Tripoli cewa, burin shugaban Faransa Emmanuel Macron shi ne ganin an taimakawa Libya fita daga cikin halin da ta tsinci kanta.

Ministan yace ziyarar ta biyo bayan wanda ya kai Libya ne ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, inda suka kulla yarjejeniyoyi tsakanin Faransa da gwamnatin dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma bangaren Jagoran kwamanda Khalifa Haftar dake gabashin kasar.

Ministan wajen na Faransa tare da takwaransa na Libya Mohammed al-Taher Siala sun ce babban abinda Faransa ke bukata shi ne abinda mutanen kasar ke bukata dama kasashen dake makwabtaka da Libyan.

Tun kawar da gwamnatin shugaba Mu’ammar Gaddafi a shekara ta 2011, kasar Libya ta fada tashin hankalin da har yanzu aka kasa warwarwewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.