rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Odinga na son a ba sauran ‘yan takara dama a zaben Kenya

media
Raila Odinga dan takarar adawa a Kenya REUTERS/Thomas Mukoya

Shugaban adawar Kenya Raila Odinga ya gindaya wasu sharudda da ya ke so a amince da su kafin shiga sabon zaben shugaban kasar da za a yi ranar 17 ga watan gobe.


Odinga ya bukaci sake wasu daga cikin jami’an hukumar zaben da kuma gurfanar da wasu a gaban kotu saboda zargin tafka magudi da kuma bai wa daukacin jam’iyyun siyasar damar sanya ranar gudanar da zaben sabanin ranar da hukumar zabe ta sanar.

Dan takarar ya kuma bukaci a ba daukacin ‘yan takarar shugaban kasar 8 izinin shiga zaben maimakon a yi zaben tsakanin shi da shugaba Uhuru Kenyatta.

A ranar Juma’a ne kotun kolin Kenya ta soke zaben Kenya da aka gudanar a ranar 8 ga Agusta, wanda shi ne karon farko da aka taba gani a Afrika.

Kotun ta tsayar da ranar 17 ga Oktoba domin gudanar da sabon zabe tsakanin shugaba Uhuru Kenyatta da babban mai hamayya da shi Raila Odinga.