Isa ga babban shafi
Afrika

Zuma zai sake fuskantar tarkon ‘Yan adawa a Afrika ta kudu

‘Yan Adawan kasar Afirka ta kudu sun kaddamar da wani sabon yunkuri na shirin tsige shugaban kasar Jacob Zuma na zuwa kotu inda suka bukaci kotun ta tilastawa Majalisar dokoki kafa kwamitin da zai binciki shugaban.

Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma
Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma PHILL MAGAKOE / AFP
Talla

‘Yan adawan sun ruga kotun kolin inda suka gabatar da bukatar ganin ta umurci Majalisar dokoki kafa kwamitin bincike kan zarge zargen cin hanci da ake yi wa shugaba Jacob Zuma.

Wannan ya biyo bayan kasa samun nasara a wata kuri’ar yankar kaunan da ‘yan adawa suka yi ta gabatar wa a zauren Majalisar.

A bara kotu ta yanke hukuncin cewar shugaba Jacob Zuma ya gaza wajen kasa kare kundin tsarin mulki musamman kan kin mayar da kudaden da ya yi amfani da su wajen fadada gidansa ta hanyar da bai kamata ba.

A wani bangare kuma, Majalisar dokokin Afirka ta kudu ta fara tafka mahawara kan bukatar Jam’iyyar Democratic Alliance na matso da zaben kasar gaba, maimakon shekarar 2019.

Dan Majalisa John Steenhuisen ya ce ba za su iya hakuri da ci gaba da shugabancin Zuma na shekaru biyu nan gaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.