Isa ga babban shafi
Togo

'Yan adawa na ci gaba da zanga zanga a Togo

Dubban masu bukatar dawo da amfani da kundin tsarin Mulkin kasar Togo na shekarar 1992 da ya takaita wa'adin shugabancin kasar sau biyu babu kari ne, yau ma suka aiwatar da wata zanga zanga inda suka fantsama kan manyan titunan Lomé babban birnin kasar. Zanga zangar ta yau na zuwa ne bayan wadda ta gudana jiya Laraba da ta hada sama da mutane dubu 1000 a manyan biranen kasar a cewar kungiyoyi masu zaman kansu.

Un homme manifeste contre le pouvoir en place du président Faure Gnassingbé à Lomé, Togo, le 6 septembre 2017.
Un homme manifeste contre le pouvoir en place du président Faure Gnassingbé à Lomé, Togo, le 6 septembre 2017. REUTERS/Noel Kokou Tadegnon
Talla

A ranar farko ta zanga zangar dubban mutane ne suka fantsama akan titunan manyan biranen kasar ta Togo 10, domin karbar kiran yan adawar na  neman tilastawa gwamnati sake mai do da tsohon kundin tsarin mulkin kasar na 1992 nan take, da ya tanadi waádin shugabancin kasa sau biyu babu kari.

Duk da amincewa da gwamnati ta ce ta yi wajen sake mai do aiki da tsohon kundin, yan adawar na ganin romon baka ne kawai,inda suka ce idan har gwamnatin da gaske ta ke kamata ya yi ta kai zance a fara tattauna shi a majalisar dokoki.

Masu zanga zangar da suka cika manyan titunan birnin na lome na dauke ne da allunan da kuma kwalaye da ke kunshe da sanarwar cewa shekaru 50 ba kwana 50 ba ne, haka kuma salon mulkin mallaka ya dai na aiki domin tura ta kai bango.

Tun a jiya ne dai Jagoran adawa a kasar Jeab-Pierre Fabre ya bukaci daukacin 'yan adawar su ci gaba da zanga-zangar don ganin bukatarsu ta biya kan dawo da amfani da tsohon kundin tsarin mulkin na 1992 da ya tanadi waádi 2 na shekaru biyar biyar.

A lokacin da ya ke tsokaci, daga birnin Abijan inda ya halarci taron bunkasa noma a Afrika Firaministan kasar ta Togo Komi Sélom Klassou, cewa ya yi bukatar 'yan adawar na nufin duk wani da aka zaba sau biyu a baya idan aka dawo da amfani da kundin tsarin mulkin na 1992 to fa bashi da hurumin sake tsayawa takara lamarin da ya ce ya sabawa doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.