rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Togo za ta tattauna batun yi wa kundin tsarin mulki gyara

media
Masu zanga-zanga a birnin Lomé, Togo, ranar 6 ga watan satumbar 2017. REUTERS/Noel Kokou Tadegnon

Majalisar dokokin kasar Togo za ta gudanar da zama na musamman a ranar talatar mai zuwa domin tattauna batun yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara domin sanya wasu daga cikin bukatun 'yan adawa da yanzu haka ke can suna gudanar da tarzoma.


Bayanai sun ce majalisar na shirin amincewa da daftarin dokar da ke bayar da damar dawo da tsohon kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1992, wanda ke kayyade wa'adin shugabancin kasar sau biyu babu kari da kuma sauran bukatun 'yan adawar da suka share tsawon kwanaki suna gudanar da zanga-zanga a birnin Lome da sauran sassan kasar.

A jiya alhamis, manzon musamman na MDD a yammacin Afrika Mohammed Ibn Chambas ya kai ziyara a kasar, inda ya gana da wakilan 'yan adawa da kuma bangaren gwamnati domin kwantar da hankula.

Lamurran dai sun tsaya cik, da suka hada da na tattalin arziki, ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu musamman a birnin Lome da wasu manyan biranen kasar ta Togo.