rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan adawar Kenya sun kafa gidauniyar taimaka wa Odinga

media
Gungun jam'iyyun adawa na Kenya dauke da hoton jagoransu, Raila Odinga SIMON MAINA / AFP

Gungun jam’iyyun adawa a Kenya sun kafa gidauniyar neman tallafin kudi daga magoya bayansu domin yakin neman zaben dan takarar adawa Raila Odinga.


Neman tallafin dai, bai rasa nasaba da rashin kudi da ‘yan adawar suka tsinci kansu a ciki bayan kashe kudi a zaben watan Agusta da kotun kolin kasar ta soke.

A watan gobe ne mutanen Kenya za su koma rumfunar zabe domin sake kada kuri’a a zaben shugaban kasa tsakanin shugaba Uhuru Kenyata da Raila Odinga.

Tuni dai shugaba Kenyatta ya fara yakin neman sake zaben sa, in da aminansa daga sassan kasar ke mara ma sa baya.