rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Yan adawa a Togo sun ki amincewa da sauye-sauyen Siyasa na Majalisar Kasar

media
Shugaba Faure Gnassingbé na kasar Togo. rfi

Shugabannin jam'iyun adawa a kasar Togo sun bayyana cewa bisa dukkan alamu ba za’a sami irin sauye-sauyen siyasa da suke bukata ba, yayinda Majalisar Kasar ke shirin fara muhawara game da chanje-chanje cikin kundin tsarin mulki, bayan an kwashe kwanaki jama’a  na bore domin ganin an sami sauye-sauyen siyasa.


Dubban masu zanga-zanga suka bazama tituna domin tilasta ganin an dibawa Shugaban kasa wa’adin iko, da kuma bukatar ganin shugabancin kasar ya fice daga gidan Shugaba Faure Gnassingbe wadanda ke mulki na kusan shekaru 50.

Shi dai shugaba Faure Gnassingbe ya maye gulbin mahaifinsa ne a shekara ta 2005, wato bayan mutuwar mahaifin na sa.

Yanzu haka dai wani mai Magana da yawun kungiyoyin adawan Eric Dupuy ya bayyana matakin majalisar kasar da cewa dabarun bata lokaci ne kawai suke shirin yi.