Mali
Mali: An kaddamar da cibiyar rundunar sojin kasashe 5
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya kaddamar da cibiyar rundunar sojin kasashe 5 da zasu yi yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel.
Wallafawa ranar:
Talla
An sanya cibiyar ne a Sevare dake tsakiyar kasar Mali, wadda ke da nisan kilomita 10 daga gabashin Mopti, a yankunan da ake fama da tashin hankali.
Rundunar mai bataliya 5, zata kunshi dakaru 5,000 da zasu fito daga kasashen Nijar, Chadi, Mali, Mauritania da kuma Burkina Faso.
Za kuma a rika warewa rundunar kasafin kudi na Dala miliyan 496 kowacce shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu