Isa ga babban shafi
DRC

Kungiyoyin Fararen hula sun gabatar da ranakun zabe

Kungiyoyin Fararen hula a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun gabatar da abin da suka kira ranakun gudanar da zabubukan kasar inda suka bukaci hukumar zabe ta amince da su.

Shugaba Joseph Kabila na DR Congo
Shugaba Joseph Kabila na DR Congo REUTERS/Yves Herman/File Photo
Talla

Kungiyoyin sun sanya ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin ranar zaben shugaban kasa, yayin da za’a gudanar da yakin neman zabe daga 1 ga watan Disamba zuwa 30 ga wata.

Jagoran kungiyoyin Abraham Djamba ya ce matakin ya biyo bayan gazawar hukumar zabe da gwamnatin kasar na sanya ranar zaben da zai kawar da shugaba Joseph Kabila daga karagar mulki.

Shugaba Kabila da ke ci gaba da na cewa kujerar mulki babu wani shirin ranakun zaben da ya sanar, duk da dai ya alkawarta gudanar da zaben sakamakon matsin da ya ke fama da shi daga 'yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.