Isa ga babban shafi
Togo

Majalisar Togo za ta fara nazari kan dokar kasar

Shugaban Majalisar Dokokin Togo Dama Dramani ya ce, gobe ne Majalisar za ta fara nazari kan bukatar sauya kundin tsarin mulkin kasar sakamakon zanga-zangar da aka samu don ganin an kawo karshen mulkin iyalan gidan shugaban kasar, Faure Gnassingbe.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faure Gnassingbé à birnin Lome
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faure Gnassingbé à birnin Lome REUTERS/Noel Kokou Tadegnon
Talla

'Yar Majalisa Isabelle Ameganvi ta ce, tafka mahawara don amincewa da sanya wa’adin shugabancin kasar ta zama wajibi kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bada shawara.

'Yan adawar kasar sun kwashe makwanni suna gudanar da zanga-zanga a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta National Alliance For Change bayan sun shafe sama da shekaru 10 suna bukatar samar da sauyi a kasar.

Ko a wannan makon zai da Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta bukaci bangarorin gwamnati da na 'yan adawa da su hada kai wajen samar da sauyi a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.