Isa ga babban shafi
Uganda

Majalisar dokokin Uganda ta jingine batun gyaran kundin tsarin mulki

Majalisar dokokin kasar Uganda, ta dakatar da muhawara kan daftarin dokar da ke neman bai wa Yuweri Museveni damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben mai zuwa, wannan kuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa wannan shiri.

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni
Shugaban Uganda, Yoweri Museveni ©Gaël Grilhot/RFI
Talla

Shugaban majalisar dokokin kasar Jacob Oulanyah, shi ne ya sanar da dakatar yin mahawarar a lokacin da yake gabatar da jawabi ga sauran ‘yan majalisar kasar a birnin Kampala, inda ya ce an yi hakan ne domin kwantar da hankula.

Oulanyah, ya ce akwai yiyuwar za a sake dawo da wannan batu domin ci gaba da mahawara a zauren majalisar a wata ranar da bai bayyana ba a nan gaba.

Masu fafutukar kare dimokuradiyya, shugabannin addinai da kuma ‘yan siyasa cikin har da wadanda ga al’ada suka saba goyon bayan Museveni da dama ne ke nuna adawa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara don bai wa shugaban damar sake tsayawa takara a zaben da za a yi a shekara ta 2021 idan Allah ya kai mu.

Yuweri Museveni mai shekaru 73 a duniya, ya share sama da shekaru 30 kan karagar mulki, to sai dai a karkashin kundin tsarin mulkin kasar da ake amfani da shi a yanzu, duk wanda shekarunsu suka wuce 75 ba zai iya tsayawa takarar shugabancin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.