rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Amurka Birtaniya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Najeriya Buhari ya bar New York zuwa birnin London

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. dailypost.ng

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar New York na kasar Amurka zuwa London da ke Birtaniya, kamar dai yadda wata sanawar daga fadar shugaban ta tabbatar.


Buhari ya halarci taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya inda ya gabatar jawabi tare da ganawa da shugabannnin kasashen duniya da dama kafin ya tashi zuwa birnin na London, to sai dai sanarwar ba ta yi Karin bayani dangane da abin da dalilan ziyara ta shugaban zuwa London ba.

 

A cikin watan agustan da ya wuce ne Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan share sama da kwanaki dari yana jinya a London, to sai dai a wannan karo babu karin bayani ko shugaban zai sake ganawa da likitocinsa ne ko kuma a’a.