Isa ga babban shafi
Zambia

Zambia na fargaba kan kwararowar 'yan gudun hijira

Kasar Zambia ta fara nuna fargaba kan dubban ‘yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwararowa kasar sakamakon rikice-rikicen da su ke ci gaba da faruwa a kasashensu. Wata sanarwa Fadar shugaban kasar na Zambia Edgar Lungu ta fitar ta sanar da cewa ko cikin watan nan kimanin 'yan gudun hijira dubu 6 ne suka tsallako kasar daga makwabta.

Zambia na ci gaba da fargabar kwararowar da baki 'yan gudun hijira ke ci gaba da yi cikin kasar don samun mafaka.
Zambia na ci gaba da fargabar kwararowar da baki 'yan gudun hijira ke ci gaba da yi cikin kasar don samun mafaka. Reuters
Talla

Galibin 'yan gudun hijirar a cewar sanarwar wadanda rikici ke i gaba da korowa ne daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, lamarin da ke tilasta musu neman mafaka a kasashen makwabta.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu a rikicin kasar na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, yayinda wasu fiye da miliyan daya suka rasa muhalli. A yankin Kasai na jamhuriyyar Democradiya ta Congo.

Yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira kusan dubu 60 a kasar ta Zambia, yawancinsu daga kasashen Angola da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da Rwanda da kasashen Burundi da Somalia da kuma Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.