rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga kan zabe a Kenya

media
‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga kan zabe a Kenya REUTERS/Baz Ratner

‘Yan sanda a kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa magoya bayan jagoran ‘yan adawa Raila Odinga da ke gudanar da zanga-zangar neman a tube illahirin manyan jami’an hukumar zaben kasar.


Dimbin magoya bayan Odinga ne suka yi cincirindo a gaban ginin hukumar zaben, a dai-dai lokacin da ya rage wata daya a sake gudanar da zaben shugabancin kasar kamar dai yadda kotun koli ta bukaci a yi.

Tun sauke zaben ake samun tashin hankali tsakanin magoya bayan shugaba Uhuru Kenyatta da ke alla-wadai da hukunci kotun da kuma magoya bayan Odinga da ke barazanar kauracewa zaben muddin ba a sauya shugabanni hukumar zaben kasar ba.

Kotun dai ta sauke zaben shugabancin kasar da aka gudanar 8 ga watan Agustan watan da ya gabata a kan kura-kuran da ta ce an tafka.