rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chadi Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jirgin Sojin Faransa ya yi hatsari a Chadi

media
Faransa na da jiragen yaki na Mirage 8 a yankin Sahel Photo: ministère de la Défense, source: Etat-major des armées

Daya daga cikin jiragen sojin Faransa da ke aikin tattara bayanan sirri da kuma fada da ayyukan ta’addanci tsakanin Nijar da kuma Chadi ya yi hatsari, inda daya cikin sojojin da ke cikinsa ya samu mummunan rauni.


Sanarwar da ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar ta ce jirgin samfurin Mirage 2000, ya tarwatse ne a lokacin da yake kokarin tashi daga barikin da ke birnin N’dajamena na Chadi.

Jirgin na shirin komawa ne zuwa Faransa

A jimilce jirage 8 ne Faransa ta mallaka a yankin na sahel 4 a N’djamena, 4 a Yamai, domin yaki da ta’addanci da dakarun Barkhane na kasar ke yi a yankin.