rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarihin Afrika Karancin Abinci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yara sama da 800,000 ke fuskantar bala’in yunwa'

media
Wasu daga cikin yaran 'yan gudun hijiran Somalia REUTERS/Thomas Mukoya

Kungiyar Agaji ta World Vision ta ce yanzu haka yara sama da 800,000 ke fuskantar bala’in yunwa a Gabashin Afirka sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma tashe tashen-hankulan da ake samu.


Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta ce tashe-tashen hankulan da ake samu a kasashen Sudan ta kudu da Somalia da kuma tsananin farin da aka samu a Gabashin Afirka sun jefa rayuwar yara kanana miliyan 15 cikin hadari, saboda rashin abinci mai gina jiki da tsabtacacen ruwan sha da samun kula da lafiya da kuma ilimi.

Kungiyar World Vision ta ce kasashen Habasha da Somalia da kuma Kenya sun fuskanci matsalar yunwa tsakanin kananan yara a cikin makwannin da suka gabata, inda yankuna da dama suka ce sama da kashi daya bisa uku na yaran su na fama da rashin lafiya.

Daraktan kungiyar a Gabashin Afirka, Christopher Hoffman, ya ce suna cikin mawuyacin hali yanzu haka ganin yadda yara sama da 800,000 ke fama da tamowa.

Daraktan ya ce muddin ba’a dauki matakin gaggawa ba akasarin yaran na iya rasa rayukan su.