MDD ta damu da tabarbarewar lamurra a Myanmar
Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana damuwarsa kan halin tabarbarewar lamurra a kasar Myanmar, inda ya bukaci kawo karshen matakan soji da gwamnati ke yi kan ‘yan kabilar Rohingya.
Wallafawa ranar:
Yayin jawabinsa ga kwamitin Sulhu, Guterres ya bayyana cewa matsalar Myanmar ta haifar da ‘yan gudun hijira sama da rabin milyan, wadanda suka tsere zuwa Bangladesh, inda ya ke cewa ba za su amince da haka ba.
Shirin kai jami’an Majalisar Dinkin Duniya zuwa Jihar Rakhine da Myanmar don gane wa idanunsu abin da ke faruwa ya rushe, bayan da gwamnatin kasar ta sauya matsayin ta a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu