Turkiya ta bude sansanin sojinta mafi girma a Somalia
Turkiya ta bude sansanin sojinta a babban birnin kasar Somalia, Mogadishu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sansanin sojin da aka bude shi a jiya Asabar, bayan kamala gininsa a kan dala miliyan 50, shi ne mafi girma da Turkiya ta taba budewa a wata kasa.
Babban Kwamandan rundunar sojin Turkiya, Hulusi Akar, yace Sama da sojojin Somalia 10,000 ne za’a horar a sansanin.
Zalika kwamandan ya ce za’a iya horar da sojoji dubu daya a lokaci guda cikin sansanin ba tare da matsi ba.
Matakin ya dada karfafa dangantakar kasashen biyu musamman ta fuskar dilfomasiya da kuma tsaro, kasancewar bude sansanin yazo a dai dai lokacinda kasar ta Somalia ke fama da hare-haren mayakan kungiyar al-Shebaab da ke neman hambarar da gwamnatin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu