rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Sandan Kenya sun tarwatsa 'yan adawa a Nairobi

media
'Yan sandan Kenya sun tarwatsa 'yan adawaa da ke zanga-zanga a birnin Nairobi REUTERS/Goran Tomasevic

Jami’an ‘yan sandan Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa-kwalla wajen tarwatsa dandazon ‘yan adawa da ke zanga-zanga a birnin Nairobi a wannan Litinin.


‘Yan adawar dai na bukatar gwamnati da ta kori jami’an hukumar zaben kasar da aka zarga da tafka magudi a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

Kazalika rahotanni sun ce, ‘yan sandan sun dauki irin wannan mataki na harba barkonon tsohuwa a yammacin birnin Kisumu.

Ana saran sake gudanar da zaben shugabancin Kenya a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba bayan Kotun Koli ta soke zaben farko da aka gudanar a cikin watan Agusta saboda kura-kuren da ta ce an samu.

Za a dai sake fafatawa tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga.