Isa ga babban shafi
Najeriya

Diezani na son ta dawo Najeriya don ta kare kanta a Kotu

Tsohuwar Ministan man fetir a Najeriya Diezani Alison-Madueke ta bukaci Kotu ta ba ta dama domin ta dawo ta kare kanta kan tuhume-tuhumen sace kudaden kasa.

Tsohuwar Ministan mai a Najeriya Diezani Alison-Madueke
Tsohuwar Ministan mai a Najeriya Diezani Alison-Madueke REUTERS/Rick Wilking/File photo
Talla

Ministar ta bukaci babbar Kotun Lagos ta ba gwamnatin Tarayya umurnin saukake mata hanyar da za ta dawo ta kare kanta.

Diezani na son kare kanta ne kan zargin ta raba kudi dala biliyan 35 ga ‘yan siyasa a jihohin Najeriya 36 domin kamfen a zaben 2015.

Hukumar EFCC ce ta shigar da kara a kotu inda ta ke zargin Dele Balgore da tsohon Ministan tsare tsare Abubakar Suleiman da karbar kudi Naira miliyan 450 daga Diezani.

Tsohuwar Ministan ta albarkatun mai a zamanin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan na fuskantar tuhume tuhume guda 4, kuma tana son kafin sake sauraren shari’ar a ba ta damar zuwa ta kare kanta.

A jiya Talata kotun Lagos ta dage sauraren karar zartar da hukunci kan tabbatar da kwace gidajen tsohuwar ministan 58 da ta saya tsakanin 2011 zuwa 2013 akan kudi sama da dala biliyan 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.