Isa ga babban shafi
Chadi

Tsutsa mai lalata amfanin gona na ta’adi a Chadi

Wata tsutsa mai lalata amfanin gona ta bayyana a wasu yankunan kasar Chadi, inda tuni ta fara yin mummunan ta’addi ga amfanin gona, almarin da ke matukar barazana ga wadatuwar abinci a kasar.

Tsutsar ta yi babban ta'adi ga amfanin gona a Kenya
Tsutsar ta yi babban ta'adi ga amfanin gona a Kenya Riccardo Gangale/Bloomberg via Getty Images
Talla

Tsutsar wadda asalinta aka ce ta fara ne a kasar Amurka, a cikin wannan shekara ta lalata dimbin amfanin gona a kasashen kudancin Afirka, kafin daga bisani ta isa kasar ta Chadi.

Malam Sanusi, wani manomi a kauyen Yarwa Baktaba, ya ce Tsutsar tun tana karama ta ke ta’adi har ta girma, kuma duk amfanin gonar da ta ci karo da shi ta ke cinyewa.

Sannan Tsutsar ta banbanta akwai mai cin amfanin gona idan ya fito, kamar gero da dawa da ta ke ci daga ciki ta mayar gari akwai kuma ta kasa da ke lalata shuka a cewar Malam Sanusi.

Yawancin mutanen kasashen Afrika dai na dogaro ne da arzikin noma.

A watan Afrilu ne Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsutsar wacce ke cinye amfanin gona ta isa kasashen Rwanda da Kenya, bayan ta’adin da ta yi a wasu kasashen da ke kudancin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.