rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zaman makoki a Nijar bayan kisan sojojin kasar

media
Shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou ISSOUF SANOGO / AFP

Gwamnatin Nijar ta kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku bayan kisan sojojinta hudu tare da na Amurka guda uku a wani harin kwantan bauna da aka kai ma su kusa da kan iya da Mali.


A ranar Laraba ne aka kai wa dakarun na hadin guiwa hari a yankin kudu masu yammacin kasar kusa da iyaka da Mali.

Sojojin Nijar kusan bakwai suka jikkata a harin da wasu guda biyu na Amurka bayan mutuwar sojojin kasasuen biyu guda bakwai.

Harin dai ya tabbatar da akwai dakarun Amurka a cikin Nijar da ke taimakawa kasar yakar ‘yan ta’adda.