Isa ga babban shafi
Nijar

Tabbas, sojin Amurka na fagen daga a Jamhuriyar Nijar

Kisan da aka yi wa dakarun Amurka uku a kusa da iyakar Nijar da Mali, na tabbatar da kasantuwar dakarun kasar a fagen daga cikin kasashen yankin Sahel.

C130-J «Hercules», mallakin Amurka a jamhuriyar Nijar
C130-J «Hercules», mallakin Amurka a jamhuriyar Nijar © RFI/Olivier Fourt
Talla

Duk da cewa tun farkon shekara ta 2000 ne aka fara ganin dakarun na Amurka a yankin karkashin wani shiri da ake kira Pan Sahel Initiative (PSI) don taimakawa a yaki ayyukan ta’addanci, to amma ba wata hujjar da ke tabbatar da cewa dakarun na shiga a fagen daga domin yaki kafada-da-kafada da dakarun kasar ta Nijar sai a wannan karo.

A shekara ta 2004 ne Amurka ta kaddamar da wani shiri mai suna Trans-Sahara Counter Terroism Intiative (TSCTI), shirin da a karkashinsa dakarun Amurka ke bai wa takrarorinsu na Nijar horo kan dubarun fada da ayyukan ta’addanci da kuma samar da makamai na zamani da za a iya amfani da su don tunkarar ‘yan ta’adda.

Tun daga wannan lokaci, a kowace shekara, sojin Amurka na gudanar da atisayen hadin gwiwa da sojin Nijar wanda ake kira Flintock.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.