rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a soma shara'ar yan Boko Haram a gobe

media
Wasu yan kungiyar Boko Haram a Najeriya RFIHAUSA/Bilyaminu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranar gobe 9 ga watan oktoba a matsayin ranar da za a fara shara’ar mutane dubu daya da 600 da ake zargin cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne da ke tsare a hannun jami’an tsaron kasar.


Sanarwar da ma’aikatar shara’ar kasar ta fitar ta bayyana tuni aka samar da alkalan da za su yi wa mutanen shara’a, sannan kuma ma’aikatar za ta samar da lauyoyi da za su kare wadanda ake zargin a gaban kotu.

Hakan na nuni ta yadda hukumomin kasar suka damu da halin da wadanan mutane suke ciki.