Isa ga babban shafi
Liberia

Al'ummar Liberia na shirin kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Al'ummar Liberia na shirin kada kuri'a a gobe Talata don zaben shugaban kasar da zai maye gurbin shugaba Ellen Johnson Sirleaf wacce ta shafe shekaru 12 tana jagorancin kasar.

'Yan takara 20 ke neman maye gurbin shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf a zaben da za a gudanar a wannan mako
'Yan takara 20 ke neman maye gurbin shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf a zaben da za a gudanar a wannan mako REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sama da mutane 20 ke takara a zaben da zai kawo karshan shugabanci Uwargida  Sirleaf, shugabar kasa mace ta farko a Afrika da ta yi kokarin farfado da kasar bayan fuskantar yake-yake a tsawon shekaru da kuma annobar Ebola da ta yi tasiri ga ci gaban kasar.

Daga cikin ‘yan takarar da sukayi fice, akwai fittacen tsohon dan wasan kwallon kafa, George Weah da mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu, Joseph Boakai, da magudun ‘yan adawa, Charles Brumskine da kuma attajirin dan kasuwa Alexander Cummings.

Sai kuma mace daya tilo wacce tauraruwa ce da ta talllata kayan adon mata, amma yanzu tana gudanar da ayyukan agaji, MacDella Cooper, wacce ake ganin ba ta da wani tagomashi.

Wata jami’ar Kungiyar Tarayyar Turai da ke sa’ido a kan shirin zaben kasar, Maria Arena ta ce zaben daya hada da na shugaban kasar da ‘yan Majalisar Dokoki, zakaran gwajin dafi ne ga Demokradiya a Liberia.

Jami’ar ta ce samun damar kammala zaben da mika mulki cikin kwanciyar hankali, abune mai muhimmaci ba ga Liberia kadai ba, har da sauran kasashen nahiyar Afrika.

Masu sharhi na tsokaci cewa wannan zabe na iya sake inganta zaman lafiya a kasar wadda ta shafe shekaru da dama tana fuskantar kazamin juyin-mulki da kuma salon mulkin kama karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.