rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnati na nazari kwace kamfanin wuta daga hannun 'yan kasuwa

media
Turken wutar lantarki a Najeriya nepa

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta sake nazari a game da kamfanin wutar lantarkin kasar da aka sayar domin ganin an inganta ayyukan kamfanonin da har yanzu suka gaza biyan bukatun ‘yan kasar.


Shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya bayyana haka wajen rufe taron tattalin arzikin kasa da aka yi a Abuja, inda ya ke cewa sake fasalin zai shafi mallakar kamfanonin da kuma tabbatar da cewar wadanda aka mika wa tafiyar da su na da karfin gudanar da su.

Bayan sayar da hannayen jarin sashen samar da wutar lantarkin, gwamnatin tarayya ta ci gaba da ware makudden kudade domin tallafa wa sashen, to amma har yanzu ‘yan Najeriya na ci gaba da korafi saboda karancin wuta a kasar.