Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Hadarin Jirgin sama ya hallaka mutum 4 a Cote D'Ivoire

Akalla mutane hudu ne suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata bayan fadowar wani jirgin sama dauke da kaya da mutane a gabar tekun Ivory Coast mai tazara kalilan da filin jirgin saman da ke Abidjan babban birnin kasar.

Jirgin Saman da ya yi hadari safiyar yau a Abidjan babban birnin Ivory Coast.
Jirgin Saman da ya yi hadari safiyar yau a Abidjan babban birnin Ivory Coast. Reuters Africa
Talla

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hadarin ya faru ne jim kadan bayan tashin jirgin lokacin da ake tsaka da maka wani kakkarfan ruwan sama mai hade da iska da kuma tsawa.

Tuni dai jami’an kashe gobara suka isa wurin da lamarin ya faru inda suka kwashe gawar wadanda suka mutu da suka kunshi mutum biyu daga cikin jirgin da kuma mutane biyu da suka makale baraguzan jirgin.

Wani ganau ya tabbatar da ganin mutane biyu da ya ce suna cikin mawuyacin hali kuma tuni aka dauke su don basu kulawar gaggawa a Asibiti.

Babu dai rahoton ko hadarin ya rutsa da mutanen da ke kasa, haka zalika kawo yanzu ba a bayyana sunan kamfanin da ya mallakin jirgin da ya yi hadarin ba.

Sai dai rahotanni na nuni da cewa dakarun sojin Faransa na amfani da filin jirgin, a yakin da su ke da mayaka masu fafutukar jihadi a kasashen yammacin yankin Sahel na Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.