Isa ga babban shafi
Somalia

Mutum 276 aka kashe a harin Mogadishu

Gwamnatin Somalia ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani kazamin harin bam ya kai 276, yayin da ta shiga zaman makoki na kwanaki 3.

Kazamin harin bam a birnin Mogadishu na Somalia
Kazamin harin bam a birnin Mogadishu na Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Shi dai wannan adadi na daya daga cikin hare-hare mafi muni da Somalia ta gani, ya tashi ne daga 20 a ranar farko zuwa sama da 270 a sa’o'i bayan kaddamar da shi.

Ibrahim Mohammed, mai Magana da yawun 'Yan Sanda, ya ce suna samun adadi masu karo da juna daga bangarorin kula da lafiya.

Sai dai ma'aikatar yadda labaran kasar ta ce mutum 276 suka mutu, yayin da wasu 300 suka jikkata, kuma wasu daga cikin su raunin nasu ya yi tsanani.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Somalia, Abshir Ahmed, ya ce sun ziyarci asibitin Madina, kuma Daraktan asibitin ya shaida musu cewar sun karbi gawawaki 218.

Shugaban kasa Mohammed Abdullahi Farmajo ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki 3 a fadin kasar.

Shugaban kasar Somalia ya bukaci hadin-kai domin yakar ta'addanci

Kasashen Duniya na ci gaba da aikewa da sakon ta’aziya ga hukumomin kasar.

Shugababn Faransa Emmanuel Macron da Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson da shugaban kungiyar kasashen Afrika ta AU Moussa Faki Mahamet duk sun yi Alla-wadai da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.