Isa ga babban shafi
Kenya

Ba mu da matsala da bukatun ‘yan adawa- Ruto

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ba ruwan gwamnatinsa  da dukkanin bukatun ‘Yan adawa da hukumar zaben kasar IEBC ta amince, illa abin da ya sa gaba shi ne tabbatar da ganin an yi zaben shugaban kasa a ranar 26.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto REUTERS/Noor Khamis
Talla

Wannan na zuwa a yayin da jagoran adawa Raila Odinga ke jiran sakamakon bukatunsa da ya shigar a gaban hukumar zaben kasar.

Mataimakin shugaban kasa William Ruto ya shaidawa RFI cewa ba su da wata matsala game da bukatun ‘yan adawa da IEBC ta amince.

“Idan sun amince akan sabbin wadanda za su buga kuri’a kai har ma da na’uzar zabe, mu ba mu da matsala” a cewar Mista Ruto.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa idan ma har ‘Yan adawar sun amince a tube Chiloba ba wani matsala ba ne.

Sai dai kuma ya ce sun fayyacewa wa IEBC cewa duk abinda ta amince tsakaninta da masu hamayya ba dole sai ta gabatar da shi ba

Jagoran adawar Kenya Raila Odinga ya dage kan sai an sauya tsarin zaben kasar baki daya, matakin da ya sa ya janye takararsa a zaben da za a sake a ranar 26 ga Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.