Isa ga babban shafi
Kamaru-RFI

An dage sauraren karar da Ahmed Abba ya daukaka a Kamaru

Sashen daukaka kara na kotun sojin Yawunde a Kamaru ya dage sauraren karar da Ahmed Abba wakilin RFI Hausa ya daukaka domin kalubalantar hukuncin daurin shekaru 10 da aka yanke akan sa.

Wakilin RFI Hausa Ahmed Abba, ya shafe sama da shekaru biyu a tsare a Kamaru
Wakilin RFI Hausa Ahmed Abba, ya shafe sama da shekaru biyu a tsare a Kamaru via facebook profile
Talla

Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba.

An share tsawon sa’o’i hudu ana sauraren bahasi daga bangaren masu kare gwamnatin Kamaru da kuma lauyoyin da ke kare Abba a zaman kotun da aka yi a yau Alhamis.

Tun a  ranar 21 ga watan Satumba ya kamata a soma shari’ar da Lauyoyin da ke kare wakilin na RFI Hausa suka daukaka, amma sai a yau aka soma Shari’a.

Abba ya share shekaru biyu a tsare a gidan yari a Kamaru, a yayin da ya ke jiran hukuncin karar da ya daukaka.

A watan Yulin bana ne Kotun sojin Kamaru ta zartar wa Ahmed Abba da hukunci bayan tuhumarsa da taimakawa ayyukan ta’addanci a aikinsa na aiko wa sashen hausa na RFI da rahotanni kan rikicin Boko Haram a yankin arewa mai nisa.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen Hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.