An fara taro kan kokarin magance rikicin wasu kasashen Afrika
Rikicin kasashen Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Burundi da kuma Sudan ta Kudu, su ne zasu mamaye taron kasashen Afirka 12 da za’ayi yau a birnin Brazzaville dake kasar Congo.
Wallafawa ranar:
Taron wanda zai gudana a karkashin kungiyar da ake kira Great Lakes zata hada da shugabannin kasashen Angola, Kenya, Rwanda, Sudan, Tanzania, Uganda da kuma Zambia.
Jami’an tsaro da suka hada da na ‘yan sanda da manyan hafsoshin soji, sai kuma ministocin harkokin wajen kasashen, sun kwashe kawanaki biyu suna tattaunawa domin shirya jadawalin da shugabanin kasashen zasu duba.
A watan yunin shekara ta 2016 ne kasashen da ke kiran yankinsu da Great Lakes a turance suka gudanar da makamancin wannan taro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu