Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Hukumar lafiya ta WHO ta soke mukamin Mugabe

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da janye nadin da ta yiwa Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a matsayin Jakadanta kan cutuka marasa saurin yaduwa.

A cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Human right watch, Mugabe bai cancanci mukamin jakadan WHO ba ganin yadda ya take hakkokin bil'adama a matakai daban-daban.
A cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Human right watch, Mugabe bai cancanci mukamin jakadan WHO ba ganin yadda ya take hakkokin bil'adama a matakai daban-daban. SEBASTIEN RIEUSSEC / AFP
Talla

Sanarwar da Dr Tedros ya fitar ta ce ta bibiyi orafe-korafen da kungiyoyi da daidaikun mutane suka yi kan nadin da aka sanar a jiya.

A cewar sabon shugaban Dr Tedros wanda ya fara shugabancin hukumar a watan Julin da ya gabata, ya ce kafin yanke matakin na dakatar da nadin sai da ya tuntube mabanbantan hukumomi a ciki da wajen Zimbabwe don tabbatar da ba a sanya siyasa cikin lamarin ba.

A jiya Asabar ne dai Dr Tedros ya sanar da nadin Robert Mugabe a matsayin jakadan hukumar ta WHO kan cutuka da ake saurin magance su, amma kuma kungiyoyi da daidaikun mutane suka rika sukan batun ciki har da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch da ta ce Mugabe ya take hakkokin bil'adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.