Isa ga babban shafi
Sahel

Kungiyar G5 Sahel za ta samu taimakon MDD

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta ziyarci yankin Sahel, ta ce ko shakka babu kasashen duniya za su taimakawa yankin domin kaddamar da rundunar G5-Sahel wadda za ta yaki ayyukan ta’addanci.

Shugabannin G5 tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron - Roch Marc Christian Kabore da Ould Abdel Aziz da Ibrahim Boubacar Keita da Idriss Deby da Mahamadou Issoufou a taron da suka gudanar a Bamako
Shugabannin G5 tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron - Roch Marc Christian Kabore da Ould Abdel Aziz da Ibrahim Boubacar Keita da Idriss Deby da Mahamadou Issoufou a taron da suka gudanar a Bamako REUTERS/Luc Gnago
Talla

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun kammala wannan ziyarar ne a Burkina Faso, a kokarin ganin an kafa rundunar wanzar da tsaro da kuma fada da ayyukan ta’addanci yankin wanda ya kunshi kasashe biyar.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya wanda ke cikin wannan tawaga Francois Delattre, ya bayyana wa manema labarai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso cewa, wannan rangadi ya ba su damar ganawa da shugabannin kasashen yankin dangane da sanin muhimmancin gaggauta kafa wannan runduna.

Kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritaniya da kuma Nijar sun yanke shawarar kafa rundunar mai suna G5-Sahel ne domin tabbatar da tsaro a yankunan iyakokinsu da yanzu haka ke fama da ayyukan ta’addanci.

Rundunar za ta kunshi dakaru dubu biyar, sai dai ana bukatar kudi yuro milyan 224 domin daukar dawainiyarta, kudaden da har yanzu bayanai ke cewa an gagara samar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.