Isa ga babban shafi
Nijar-Amurka

Amurka ba ta da niyyar janye dakarunta a Nijar

Amurka ta ce ba ta da niyyar janye dakarunta da ke fada da ayyukan ta’addanci daga jamhuriyar Nijar, duk da harin da aka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar hudu daga cikinsu kusa da iyakar kasar da Mali a farkon wannan wata.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Babban kwamandan askarawan kasar ta Amurka, wanda ke amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar dattawan kasar kan wannan batu, ya ce lamarin ba zai kasance hujjar janye dakarun da yawansu ya haura 800 da ke jibge a jamhuriyar ta Nijar ba.

A ranar 4 ga wannan wata na Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka kai harin kwanton bauna a kan ayarin sojojin Nijar da na Amurka da ke sintiri kusa da iyaka da Mali, inda sojojin Nijar da na Amurka suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.