Isa ga babban shafi
Sahel

Rundunar G5 Sahel ta soma aiki

Kasar Faransa ta ce rundunar kasashen Afirka da aka kafa a Yankin Sahel domin yaki da ‘yan ta’adda ta fara aiki wannan larabar.

Rundunar G5 sahel ta soma aiki
Rundunar G5 sahel ta soma aiki AFP/Stephane de Sakutin
Talla

Wani sojin Faransa Kanar Marc-Antoine da ke aiki a Mali, ya ce tun safiyar wannan larabar aka fara girke sojojin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso domin gudanar da aikin.

Jami’in ya ce tuni aka girke daruruwan sojoji a matakin farko daga cikin sojoji 5,000 da ake saran za suyi aikin.

Kasar Faransa na da dakaru akalla 4,000 a Mali domin samar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.