rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Salva Kiir Sudan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kiir ya zargi Sudan da bai wa ‘yan tawaye makamai

media
Shugaban Kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Jok Solomon

Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir ya zargi Sudan a matsayin kasar da ta zama hanyar samun makaman da 'yan tawayen kasar sa ke amfani da su wajen kai hare-hare a yakin basasar da ya hallaka dubban fararen hula.


Yayin jawabi ga manema labarai bayan tattaunawa da shugaba Omar Hassan Al Bashir a Khartoum, shugaba Kiir ya ce inda akwai wanda zai zargi wani kan safarar makaman da ake yaki da su a Sudan ta kudu, toh shi ne zai zargi kasar Sudan.

Shugabannin biyu sun tattauna kan yadda za’a magance wannan matsalar da ta jefa kasar sa cikin tashin hankali.

Duban mutane suka rasa rayukansu a yakin basasar Sudan ta kudu da ya barke a Disamban 2013, kasa da shekaru 3 da samun 'yanci daga Sudan ta Arewa.