Amurka zata yi amfani da jiragen ta a Nijar
Kasar Amurka ta samu amincewar hukumomin Nijar a karon farko na yi amfani da jiragen ta masu sarrafa kan su wajen kakkabe yan ta’adda kama daga kan iyaka da Libya zuwa arewacin Mali.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da Ministan tsaron Nijar Kalla Moutari ya tabbatar, Ministan ya bayyana cewa hukumomin Nijar sun dau wannan mataki ne kafin kazamin harin Tongo-Tongo da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin Amurka da na Nijar.
Wasu kungiyoyi masu zaman kan su a Nijar dama wajen kasar sun soma nuna damuwar su a kai , wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa baiwa Amurka damar yi amfani da jiragen ta masu sarafa kan su a sararin samaniya na tattare da hatsari ga rayuwar farraren hula musaman manoma da makiyaya dake rayuwa a karkara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu