rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka zata yi amfani da jiragenta marasa matuka a Nijar a yaki da yan ta'adda

media
Jirgin yaki mai sarrafa kan shi rfi

Gwamnatin Nijar ta sanar a hukumance cewa, ta amince Amurka ta yi amfani da jiragenta marasa matuka da ke dauke da makamai domin kai wa ‘yan ta’adda farmaki a cikin kasar.


A zantawarsa da manema labarai, ministan tsaro Kalla Moutari, ya ce sun jima suna tattaunawa da Amurka dangane da wannan batu, ba wai sai lokacin da aka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun na Amurka kusa da iyakar kasar da Mali a cikin watan jiya ba.