Isa ga babban shafi
Nijar

Amnesty internationnal ta yi kira zuwa Gwamnatin Nijar

Kungiyar Amnesty Internationnal ta yi kira zuwa Hukumomin Nijar don gani sun sako wasu shugabanin kungiyoyin farraren hula uku da ake tsare da su .

Tambarin kungiyar Amnesty Internationnal
Tambarin kungiyar Amnesty Internationnal
Talla

Mutanen da ake tsare da su, sun hada da Abass Abdoul Aziz Tanko, Abdoulaye Harouna da Djibo Issa dukkanin su wadanda aka kama yan lokuta bayan wata zanga-zangar nuna adawa da kasafin kudin shekarar 2018 da Gwamnatin kasar ta sanar.

A cewar kungiyar ta Amnesty Internationnal hukumomin suna sane da kama wasu mutane kusan 20 a ranar 29 ga watan Oktoban, daga cikin su akwai yara kanana shida, wadanan mutanen za su bayyana gaban kotu a ranar 17 ga watan Nuwemba, kungiyar ta Amnesty ta bukaci hukumomin kasar sun gaggauta salamar wadanan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.