rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mawakin zamani Wizkid ne ya lashe awards uku na Afrima

media
Wizkid mawakin zamani daga Najeriya -rfi hausa Issa -rfi hausa

Fitattun mawakan Afrika sama da 150 ne suka halarci bikin karrama mawakan nahiyar, da ake yi wa taken AFRIMA, a jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Mawaka da dama ne aka karama  a wannan gangami na Lagas.


Yayinda yake jawabi a lokacin rufe taron, Akon, mawaki dan kasar Senagal, ya ce bikin karrama mawakan na shekarar bana, zai zama madogara ga ilahirin mawakan nahiyar, kasancewar lokaci ya yi da mawakan Afrika za su amfana da aikin da suke yi.

Daga cikin mawakan da suka samu lambar yabo akwai Toofan na kasar Togo,Ali Kiba daga Tanzania,Gilad Milo daga Kenya,2Baba daga Najeriya.

Mawaki zamani Wizkid ne ya lashe awards kusan guda uku wanda hakan ke ba shi damar zama mawakin Afrika na shekarar 2017.

A daya wajen an karama wasu tsofin mawaka na Afrika da suka hada da Salif Keita na Senegal, Olivier Mutikudzi daga Zimbabwe.